Menene Web3? Cikakken Bayani Cikin Hausa (2026 Guide)
Bismillahir Rahmanir Rahim
Assalamu Alaikum.
Idan kana yawan jin ana maganar Web3, wataƙila kana tambayar kanka: Mene ne Web3?
Web3 sabon salo ne na amfani da intanet wanda yake amfani da blockchain, cryptocurrency, da wallet domin ba masu amfani cikakken iko akan bayanansu da dukiyoyinsu.
Menene Web3?
Web3 shi ne sabon ƙarni na intanet wanda aka gina akan fasahar blockchain.
A Web3, kai ne kake da iko akan bayananka da kuɗinka, ba kamar tsohon tsarin da manyan kamfanoni suke da cikakken iko ba.
Bambancin Web1, Web2 da Web3
Web1
Karanta bayanai kawai.
Ba a cika yin mu'amala ba.
Web2
Ana karantawa kuma ana rubutawa.
Social Media kamar Facebook, X (Twitter), Instagram da YouTube sun shahara.
Kamfanoni ne ke sarrafa bayanai.
Web3
Ana amfani da blockchain.
Kai ne mamallakin bayananka.
Ana amfani da Wallet wajen shiga Apps.
Ana amfani da Cryptocurrency wajen biyan kuɗi.
Muhimman Abubuwan Web3
Blockchain
Wallet
Smart Contracts
DApps (Decentralized Applications)
DeFi
NFTs
DAOs
Fa'idodin Web3
✅ Karin tsaro.
✅ Kai ne mamallakin bayananka.
✅ Babu buƙatar banki wajen wasu mu'amaloli.
✅ Sauƙin amfani da cryptocurrency.
✅ Sabbin damar samun kuɗi ta hanyar Web3.
Matsalolin Web3
Sabuwar fasaha ce.
Akwai masu damfara.
Idan ka rasa Seed Phrase, za ka iya rasa wallet ɗinka.
Wasu Apps suna da wahalar amfani ga masu farawa.
Misalan Web3 Apps
Uniswap
OpenSea
Aave
MetaMask
Trust Wallet
Kammalawa
Web3 yana canza yadda mutane ke amfani da intanet ta hanyar ba su iko akan bayanansu da dukiyoyinsu. Yana amfani da blockchain domin samar da tsaro da gaskiya a mu'amaloli.
Internet Ikon Allah Global Links and E-Connection Solutions in Collaboration with Habaglos Info-Tech

Comments
Post a Comment