Menene Stablecoin? Cikakken Bayani Cikin Hausa (2026
Bismillahir Rahmanir Rahim
Assalamu Alaikum.
Idan kana amfani da cryptocurrency, tabbas ka taɓa jin ana ambaton USDT, USDC, ko DAI. Waɗannan ana kiransu Stablecoins.
Menene Stablecoin?
Stablecoin wani nau'in cryptocurrency ne da aka ƙera domin farashinsa ya kasance kusan daidai da kuɗin ƙasa kamar Dalar Amurka (USD).
Misali:
1 USDT ≈ $1
1 USDC ≈ $1
Saboda haka, Stablecoin ba ya yawan tashi ko faɗuwa kamar Bitcoin ko Ethereum.
Amfanin Stablecoin
Ajiye kuɗi ba tare da tsananin canjin farashi ba.
Sauƙin aika kuɗi tsakanin wallets.
Yin ciniki (trading) cikin sauƙi.
Kare riba lokacin da kasuwa ta faɗi.
Mafi Shahararrun Stablecoins
USDT (Tether)
USDC (USD Coin)
DAI
FDUSD
Habaglos Info-Tech in Collaboration with Internet Ikon Allah Global Links and E-Connection Solutions

Comments
Post a Comment