Menene Blockchain? Cikakken Bayani ga Masu Farawa (2026 Guide)



 Bismillahir Rahmanir Rahim.

Assalamu Alaikum.

Idan kana son fahimtar cryptocurrency sosai, dole ne ka fara fahimtar Blockchain. Blockchain ita ce fasahar da ke sa Bitcoin, Ethereum da sauran cryptocurrencies su yi aiki cikin aminci.

Menene Blockchain?

Blockchain wata babbar ma'ajiyar bayanai ce ta dijital da ke adana dukkan bayanan ma'amaloli (transactions). Ana haɗa bayanan cikin blocks, sannan kowane block yana haɗuwa da wanda ya gabace shi, shi ya sa ake kiranta Blockchain (sarkar blocks).

Yaya Blockchain Ke Aiki?

Lokacin da mutum ya aika cryptocurrency:

Ana ƙirƙirar transaction.

. Ana tantance transaction ɗin ta hanyar kwamfutoci da ke cikin network.

. Bayan an tabbatar, ana saka transaction ɗin cikin sabon block.

. Ana haɗa sabon block ɗin da sauran blocks.

. Transaction ɗin ya zama na dindindin kuma ba za a iya canzawa cikin sauƙi ba.

Fa'idodin Blockchain

. Tsaro mai ƙarfi

. Bayyananniyar ma'amala (Transparency).

. Ba a iya sauya bayanai cikin sauƙi.

Babu buƙatar wani banki ya tabbatar da kowace ma'amala.

Ana amfani da ita a ƙasashe daban-daban.

Ana Amfani da Blockchain A Ina?

Ba cryptocurrency kaɗai ba, ana amfani da Blockchain a:

1. Kuɗin dijital.

2. Bankuna.

3. Kiwon lafiya.

4. Sufuri.

5. Kasuwanci.

6. Tsarin kwangiloli na dijital (Smart Contracts).

Shin Blockchain Lafiya Ce?

Eh, Blockchain tana daga cikin fasahohin da suka fi ƙarfin tsaro a duniya. Amma mai amfani dole ne ya kare wallet ɗinsa, PIN da Secret Phrase, domin idan waɗannan suka faɗa hannun ɓarawo, zai iya rasa kuɗinsa.

Kammalawa

Blockchain ita ce ginshiƙin cryptocurrency. Idan ka fahimci yadda take aiki, zai fi maka sauƙin fahimtar Bitcoin, Ethereum, USDT da sauran cryptocurrencies.

Habaglos Info-Tech 

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Menene Crypto Wallet Address? Cikakken Bayani Cikin Hausa (2026 Guide)

Menene DApp (Decentralized Application)? Cikakken Bayani Cikin Hausa (2026 Guide)

Menene Cryptocurrency ?